Obasanjo Da Abdussalam Za Su Ziyarci Buhari Don Sanin Halin Rashin Lafiyar Sa Tsoffin shugabannin Najeriya Olusegun Obasanjo da Abdussalam Abubakar sun yanke shawarar ziyartar shugaban kasa Muhammadu Buhari domin sanin hakikanin halin lafiyar sa. 
Wannan ya biyo bayan ganawar sirri da suka yi jiya Litinin a gidan tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida. Sai dai shi ba zai samu damar zuwa ba saboda rashin cikakkiyar lafiya.

You may also like