Obasanjo da Jonathan sun zauna kusa da juna a coci 


Toshon shugaban ƙasa Gudluck Jonathan da Olusegun Obasanjo sun zauna kusa da juna a cocin Angalika ta Saint Stephen dake Otuoke a jihar Bayelsa, a ranar Lahadi.

Dukkannin mutanen biyu mabiya ɗarikar cocin Angalika ne.

Seriake Dickson gwamnan jihar da kuma wasu manyan jami’an gwamnatin Bayelsa sun bi sahun tsofaffin shugabannin a yayin addu’ar ta yau Lahadi,ƙarƙashin jagorancin, James Oruwori babban bishop na ƙaramar hukumar Ogbia.
Ya yin da yake wa Obasanjo maraba da zuwa cocin garinsu, Jonathan yace Obasanjo ya yi alkawarin kawo ziyara Otuoke saboda ziyarar da na kai garinsu.

Jonathan yace bashi da masaniyar cewa ziyarar zata kasance da wuri haka.

Tsohon shugaban ya yi kira a samu zaman lafiya da kuma fahimtar juna a tsakanin ƴan Najeriya.

Da yake miƙa sakonsa na fatan alheri Obasanjo ya bayyana Jonathan a matsayin tsohon shugaban kasar Najeriya mafi ƙarancin shekaru.

You may also like