Obasanjo Ya Caccaki Gwamnatin Buhari


Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya furta wadansu kalamai da ke nuni da cewa ya soma dawowa daga rakiyar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

A lokacin da yake jawabi a wajen wani taro na farko don tunawa da Akintola Williams, Obasanjo ya soki gwamnatin Buhari saboda yadda take yi wa gwamnatoci ukun da suka gabata, ciki har da ta Obasanjo, kudin goro wajen zargin rashin iya jagoranci.
Ya kuma bai wa Buhari shawara da ya daina korafi kan abin da ya wuce, inda ya ce tun da an zabe shi ne domin ya gyara Nijeriya, ya kamata ya mayar da hankali kan gyara barnar da ya tarar.
Obasanjo ya kara da cewa “Cin zabe abu ne mai sauki idan aka kwatanta da gyara wata barna da aka tafka. Idan kana daga gefe abin da kake iya hangowa ba zai taba kamo kafar abin da ke nan a zahiri ba”.
Haka kuma Obasanjo ya soki shirin da gwamnatin Buhari ke yi na ciwo bashin dala biliyon 30.

You may also like