Obasanjo Ya  Nemi   Buhari Da Ya Tattauna Da Nmandi Kanu 


Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yace shugaban kasa Muhammad Buhari dole ya tattauna da Nmandi Kanu shugaban kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra.

“Ban ga wani aibu ba idan Buhari ya gana da Nmandi Kanu bazan soki lamarin yin hakan ba, a takaice zanso a ce hakan ta faru, “yace. 

Da yake magana da jaridar Newsweek  Obasanjo wanda lokacin da yake shugaban kasa ya gana da yan ta’addar yankin Niger Delta domin dakatar dasu daga fasa bututun mai yace:” Ina so na gana da Kanu da kaina nayi magana da shi naji meye damuwarsa bawai akan yankin kudu maso gabas ba kadai a kan Najeriya baki daya.”

Yace kasancewar sojoji a yankin  a matsayina martani ga masu fafutukar ba shine mafuta ba. 

Ana dai zargin sojoji da taka hakkin bil-adama tun lokacin da suka kaddamar da atisayen da suke yi a yankin zargin da suka musalta 

You may also like