Obasanjo ya zama tamkar ɗan baƙin ciki – Fadar Shugaban Najeriya..

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Fadar Shugaban Najeriya ta mayar da kakkausan martani kan kalaman da Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi a saƙonsa na sabuwar shekara.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya fitar, sanarwar ta ce Obasanjo ba zai taɓa daina caccakar Shugaba Muhammadu Buhari ba sakamakon Obasanjon ba zai daina baƙin ciki kan duk wani wanda ya sha gabansa a ayyukan ci gaban ƙasa ba.

Fadar shugaban ƙasar ta buga misali da cewa Shugaba Buhari ya kammala gadar Neja ta biyu bayan an yi shekara 30 ana alƙawura a kanta.

Haka kuma fadar shugaban ƙasar ta ce Obasanjo ya yi wa kudu maso gabashin Najeriya ƙarya domin ya samu ƙuri’unsu, amma Shugaba Buhari bai samu ƙuri’unsu ba amma duk da haka sai da ya yi musu aikin gadar.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like