Obasanjo ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa Gudluck Jonathan  a Otuoke 


Toshon shugaban kasa,Cif Olusegun Obasanjo ya ziyarci tsohon shugaban Gudluck Jonathan a gidansa dake mahaifarsa ta Otuoke a jihar Bayelsa.

Tun farkon da fari tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya isa Yenagoa babban birnin jihar a wata ziyarar aiki ta kwanaki uku da yakai   a wani ɓangare na bikin cikar gwamnan jihar Seriake Dickson shekara 6 da kama aiki a matsayin gwamna.

Obasanjo wanda ya samu rakiyar gwamna Dickson zuwa  Otuoke bayan da ya ƙaddamar da wasu aiyuka ciki har wani asibitin kwararru da kuma dakin shan magani,  ya samu tarba daga tsohon shugaban tare da mai dakinsa uwargida Patience Jonathan.

Wannan ziyara da Obasanjo ya kai Otuoke ita ce irinta ta farko tun bayan zaɓen 2015 inda ya fito fili ƙarara ya nuna adawarsa ga kasancewar Gudluck Jonathan a matsayin ɗan takarar jam’iyar PDP,har ta kai ga ya keta katinsa na jam’iyar PDP.

 Masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin cewa Obasanjo ya kai ziyarar ne a ƙoƙarin da yake na shiryawa da mutanen da ya sabawa a baya domin tunkarar shirin da yake na hana shugaban ƙasa Buhari cin zaɓe a karo na biyu.

You may also like