Obasanjo Yace Zai Sake Rubuta Wata Wasiƙar Game da Abinda Ke Faruwa A Najeriya


Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa irin yadda abubuwa ke tafiya a kasarnan ba suyi masa dadai
don haka yana tunanin kara rubuta wata wasika irin wadda ya rubuta a kwanakin baya yana caccakar gwamnatin shugaba Buhari akan salon mulkinta , Abinda ya dauki hankula sosai.

Obasanjo ya bayyana hakane a garin Legas a wurin wani taro akan cigaban mata, kamar yanda jaridar Vanguard ta ruwaito,
ya kara da cewa idan ya rubuta wannan wasikar zai jima be kara rubuta wata ba.

Obasanjo ya kuma bayyana cewa, kungiyar da ya bude dan ceto Najeriya daga halin ha’ula’in da take ciki ta samu mutane miliyan uku da suka yi rigista haddashi don haka ya nuna farin cikin sa da wannan cigaba da suka samu.

You may also like