Obaseki ya bada umarnin kama wasu ma’aikata biyu na  kamfanin BUA 


Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bada umarnin kama wasu ma’aikata biyu na kamfanin BUA kan zargin karya dokar dakatar da aiki, da suka yi  wacce ma’aikatar ma’adanai da karafa ta jihar tayi.

An bayar da umarnin ne saboda rikici da aka samu tsakanin kamfanonin BUA da kuma Dangote kan wanda ya mallaki wurin haƙar ma’adanai na Obu dake jihar.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Ƙasa NAN lokacin da gwamnan ya ziyarci wurin a ranar Laraba ya iske ma’aikata na cigaba da aiki.

“Umarnin zai cigaba ne har zuwa lokacin da kotu zata yanke hukunci kan waye ya mallaki wurin haƙar ma’adanan,” ya ce.

Obaseki ya samu rakiyar sojoji yan’sanda  da kuma jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS.

Obaseki yace gwamnatin jihar tafi mai da hankali kan tsaron rayuka da kuma dukiya idan dai har akwai bukatar masu zuba jari su mayar da kudinsu to babu dukiyar  da tafi rayukan jama’a muhimmanci.
Kamfanin Dangote da na BUA sun shiga rikici ne kan batun mallakar wurin haƙar ma’adanin da ake kira Lime Stone a turance wanda shine ake sarrafawa ya zama siminti.

You may also like