Obiano ya lashe zaɓen gwamnan Anambra


Willie Obiano ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra.

Obiano wanda shine gwamnan dake kan kujerar mulki,  ya lashe zaben ne  a karo na biyu bayan da yayi nasara a dukkanin kananan hukumomi  21 dake jihar.

Obiano wanda yayi takara a jam’iyar APGA ya samu nasara akan Tony Nwoye na APC, Oseleka Obaze na Jam’iyar PDP da kuma Osita Chidoka na jam’iyar UPP.

Dan takarar APGA ya samu kuri’a 234,071 yayin da Nwoye yazo na biyuu da kuri’a 98,572 yayin da Obaze yazo na uku da kuri’a 70,593 Osita Chidoka shine na huɗu da kuri’a 7,746.
Yan takara 37 ne suka shiga zaɓen na neman darewa kujerar mulkin jihar.

Zaɓen dai ya gudana lafiya sai dai an samu kwacen akwatunan zabe a wasu cibiyoyin zaɓe da kuma yadda wasu yan siyasar suka rika siyan kuri’a.

You may also like