A cikin wani bayani da ofishin jakadancin na Amurka ya nuna damuwarsa akan kisan da aka yi wa ‘yan shi’ar a kano da ke arewacin aksar.
Ofishin Jakadancin Amruka a Najeriya ya nuna damuwarsa akan kisan da gwamnatin kasar ta ke yi wa ‘yan shi’a.
A cikin wani bayani da ofishin jakadancin na Amurka ya nuna damuwarsa akan kisan da aka yi wa ‘yan shi’ar a kano da ke arewacin aksar.
Bayanin na Ofishin jakadacin Amurkan ya zargi jam’an tsaron kasar da amfani da karfin da ya wuce kima akan ‘yan shi’ar da su ke tattakin zuwa Zaria.
Bugu da kari, wani sashe na bayanin ofishin jakadanin Amurkan a birnin Abuja ya ci gaba da cewa; Tamkar sauran, al’ummar Najeriya, su ma ‘yan shi’ar suna da hakkin yin addininsu, daga cikin hadda yin tattaki,kuma dole ne gwamnatin kasar ta basu kariya.
A ranar litinin din da ta gabata ne dai ‘yan sandan Najeriya a jahar kano su ka bude wuta akan ‘yan shi’a da su ke tattakin arba’in akan hanyarsu ta zuwa Zaria.
Adadin mutanen da su kwata dama sun kai 100, daga cikinsu hadda mata da kananan yara.