Ofishin Kamfen Obi Ya Nuna Damuwa Kan Zargin Cin Amanar Kasa Da Gwamnati Ta Yi Wa Obin
Wannan ya biyo bayan bayanan ministan labaru Lai Mohammed a Amurka cewa kalaman Peter Obi kan sam ba daidai ne a rantsar da Bola Tinubu a 29 ga Mayu ba, don bai lashe zabe ba, ya zama cin amanar kasa, don hakan zai iya tunzura jama’a su tada fitina.

Tun gabanin bayanan na Lai Mohammed da ke nuna matsayar gwamnatin Najeriya, tuni hukumar NBC ta ci tarar gidan talabijin na Channels Naira miliyan 5 don zantawa da mataimakin dan takarar Leba Datti Baba Ahmed da shi ma ke nuna rashin dacewar rantsar da Tinubu.

Shi kan sa Peter Obi ya yi watsi da zargin da nuna takaicin cewa wasu na neman bata masa suna kuma musamman a ce da irin ministan labaru kan abun da ya ce karbuwa da ya samu; ya na mai musanta faifan sauti da ya fito da zantawar sa da shugaban majami’ar WINNERS, Pastor Oyedepo inda a ka ji Obin na zaiyana zaben da ya gabata a matsayin yakin addini.

Kakakin kamfen din Yunusa Tanko ya karfafa bayanan na Obi amma ya ce in ma laifi ne kowane bangare ya aikata irin hakan.

Shin zargin mutum da cin manar kasa ya wadatar ko akwai abun da gwamnati ta kan yi daga baya bisa tanadin tsarin mulki?

Lauyan tsarin mulki Mainasara Kogo Umar ya ce hakan ya rage ga mataki ne na gwamnati don ita ce ta kawo zargin kuma ita ke da hurumin daukar mataki, amma ba gwamnati a duniya da ke sako-sako ga batu da ya shafi zargin cin amanar kasa.

A nan Yunusa Tanko ya bukaci jami’an tsaro su tono wadanda su ka yi kwarmaton hirar salula ta Obi don ya na ganin su ke neman tada fitinar.

Za a jira a ga mataki na gaba na gwamnatin da zuwa yanzu zargi ne kadai ta ambata yayin da Obi, Atiku na PDP da jam’iyyar APM ke neman kotu to soke nasarar Tinubu da nuna an yi rufa-rufa a zaben.

Ga sautin rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like