Olisa Metuh Ya Ƙi Bayyana Gaban Kotu Bisa Zargin Karkatar Da Milyan 400


Wata kotu dake zamanta a Abuja karkashin mai shari’a Okon Abang ta dage shari’ar da take wa tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar PDP Olisa Metuh da kamfaninsa mai suna (Destra Investments Limited) kan zargin karkatar N400m ba bisa ka’ida ba a shekarar 2015.

Yayin da yake dage shari’ar zuwa 2 ga wata Yulin wannan shekarar mai shari’a Abang ya ce, “dole tasa za a dage shari’ar, saboda wanda ake zargi bai bayyana a gaban kotun ba yayin zaman shari’ar kuma lauyoyinsa basu bada wasu kwararan hujjoji ba na kin bayyanarsa a gaban kotun ba “.

Karar da aka shigar da ita tun 19 ga watan Janairun wannan shekarar aka kuma fara zaman sauraren ta ranar 25 ga watan Janairun ta ki zuwa karshe ne sakamakon yawan daga shari’ar da ake yi bisa rashin cikakkakun hujjoji da shaidu.

Gwamnati dai na karar Metuh ne bisa zarginsa da yi wa N400m rabon karta tsakanin aljihunsa, da kuma kamfanin sa mai suna (Destra Investments Limited) da ya karba a shekarar 2015 a hannun mai bai wa tsohon Shugaban Kasa Jonathan shawara a fannin tsaro Kanar Sambo Dasuki.

You may also like