Ovie Omo-Agege,sanata mai wakiltar mazabar Delta ta tsakiya ya gaza halartar zaman majalisar dattawa na yau Talata.
An tsaurara matakan tsaro a majalisar bayan da ake sa ran dawowarsa a yau.
An dakatar da sanatan na tsawon kwanakin zaman majalisar 90 bayan da ya kai majalisar dattawan kara gaban kotu.Akwai jita-jitar cewa za a iya dakatar da shi saboda adawar da ya nuna ga kudirin sauya tsarin jadawalin zabukan shekarar 2019.
Sanatan da kuma wasu sanatoci 9 sun kafe cewa dokar zaben an samar da ita ne domin a yiwa shugaban kasa Muhammad Buhari zagon kasa.
Bayan an dakatar da shi Omo-Agege ya jagoranci wasu yan daba zuwa majalisar inda suka yi awon gaba da sandar majalisar.
Duk da cewa yan sanda sun kama shi kuma suka sake shi daga baya sanatan ya musalta cewa yana da hannu a sace sandar.
Daga baya ya garzaya kotu inda ya nemi kotun ta hana jami’an hukumar DSS da na yan sanda da kada su kama shi.
A makon da ya wuce wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta soke dakatarwar da majalisar dattawan ta yi masa inda ta ce ta saba doka.