Orji Kalu Ya Nemi Da Abarshi Ya Fallasa Obasanjo Kan Wasikar Daya Rubutawa Buhari


Tsohon Gwamnan jihar Abia, Orji Ozor Kalu ya bayyana cewa a kyale shi da tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasonjo kan wasikar da rubutawa Shugaba Buhari inda tsohon gwamnan ya nuna cewa shi zai fallasa miyagun laifukan Obasonjo.

Tsohon Gwamnan ya ce, yana da hujjoji kan yadda Cif Obasonjo ya karkatar da dala Bilyan 16 da sunan aikin samar da hasken wutar lantarki a zamanin mulkinsa inda ya nuna cewa tsohon Shugaban kasar ya aikata laifukan rashawa da dama a zamaninsa.

You may also like