Ortom ya bayyana dalilinsa na kin zuwa tarbar Buhari a jihar Nassarawa


Gwamna Samuel Ortom ya yi ƙarin haske kan dalilan da suka sa shi ƙin zuwa jihar Nassarawa mai maƙotaka da jihar domin tarbar shugaban ƙasa Muhammad Buhari a ranar Talata.

Da yawa daga cikin masu lura da al’amuran yau da kullum sun nuna mamakinsu kan meye dalilin da yasa Ortom bai je ya tarbi Buhari ba amma ya tura mataimakin shi,Benson Abounu  ya wakilce shi.

Ortom cikin wani martani da ya mayar ga masu mamakin matakin nasa ya ce ba zai iya barin mutanensa ba swaɗanda fulani suke kashewa a kullum, domin yaje ya tarbi shugaban ƙasa.

Ya ce”na samu gayyata daga abokin aikina na jihar Nassarawa kan ziyarar shugaban ƙasa.domin girmamawa ga ofishinsa dana shugaban ƙasa.Na tura mataimaki na ya wakilce ni saboda bazan iya barin jihata ba alhalin ana kashe mutane na.”

A  ranar Talata ne shugaban kasa Muhammad Buhari ya kai ziyarar aiki zuwa jihar Nassarawa inda ya buɗe wasu manyan aiyuka ciki har da ginin  babbar kasuwar duniya dake Karu.

You may also like