Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya aiyana dokar hana fita a garin Gboko dake ƙaramar hukumar Gboko ta jihar inda aka kona wasu mutane 7 da ake kyautata zaton Fulani makiyaya ne.
Lamarin dai ya jefa shakku da fargaba a zukatan mazauna garin.
Da yake magana kan lamarin Moses Yamu mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta jihar yace ɓatagarin matasa dake garin sune suka kai harin.
“Hatsaniya ce a babbar tashar mota dake garin. Ƴan sanda sun yi gaggawar zuwa wurin amma suna isa sai suka iske mutane 7 maza waɗanda ba a iya gane asalinsu ba amma ana kyautata zaton ƴan ƙabilar Fulani ne, an kashe su kuma matasan dake Gboko sun cinnawa gawar su wuta,” ya ce.
Jaridar the Cable ta gano cewa wasu daga cikin mutanen da aka kashe sun zo tashar motar ne domin tafiya zuwa garin Okene a jihar Kogi wasu kuma zuwa Jihar Taraba.
Fatai Owoseni kwamishinan ƴan sandan jihar yace wasu mutane sun jikkata ba harin.
A wata sanarwa da Terhav Agerzua mai magana da yawun gwamnan ya fitar, gwamnan ya umarci jami’an tsaro kan su kasance a wurare masu muhimmanci dake yankin domin gudun domin gudun karyewar doka da oda.
Gwamnan ya roƙi mutanen garin kan su girmama dokar hana fitar.