Osinbajo da Iyalinsa sun tafi hutu Dubai


Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da kuma iyalinsa yanzu haka na can birnin Dubai na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Laolu Akande, mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasar shine ya bayyana haka cikin wani sakon Tweeter da ya wallafa.

Akande yaƙi bayyana lokacin da Osinbajo ya bar gida Najeriya ba. 

“Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, matarsa da kuma yayansa  suna hutawa a ƙasar waje a hutunsa na karshen shekara da ya saba yi,”ya rubuta.

“An sa ran zai dawo kasarnan a karshen mako daga ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.”

You may also like