Osinbajo Ya Baiwa Dangote Da Wasu Mutane 35 Sabbin MukamaiMukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ya nada masu baiwa gwamnati shawaraa kan manufofin kasuwanci a Nijeriya.

Majalasin masu bada shawarar ya kunshi mambobi 36 da suka fito daga bangaren gwamnati da bagaren ‘yan kasuwa masu zaman kan su da kuma kwamitin kwararru.

Ana tsammanin cewa mambobin majalasin za su taimakawa kasar wajen kirkirowa tare da kula da manufofin gwamnati wadanda za su habaka bangaren kasuwanci.

An yi bikin kaddamar da masu bada shawaran a jiya Talata a fadar gwamnati da ke Abuja.

Wadanda majalasin ya kunsa sun hada da mukaddashi shugaban kasa,Farfesa Yemi Osinbanjo a matsayin shugaba,  sai shugaban rukunonin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, Ministar kudi ta Nijeriya Kemi Adeosun, Ministan kasuwanci da zuba jari Dr. Okechukwu Enelamah,  shugaban rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdulsamad Rabiu, shugaban kamfanonin Nigerian Breweries da PZ Cusson chief Kola Jamoduda sauran su.

You may also like