Tsohon Gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sherif, ya gana da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa ta Aso Rock dake Abuja.
Sherif wanda tsohon dan jam’iyar APC ne,kafin ya sauya sheka zuwa jam’iyar PDP, amma a kwanakin baya kotun koli ta koreshi daga kan kujerar shugabancin jam’iyar ta PDP, yadai isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 3:20 na rana.
An dai rawaito cewa reshen jam’iyar APC na jihar Borno sun nemi da sherif ya dawo cikinsu zargin da jam’iyar reshen jihar ta Borno ta musalta.
Osinbajo ya fara ganawa da Sherif bayan da ya kammala jagoranta taron majalisar lura da tattalin arzikin kasa.
An tsaka da gudanar da taron ne aka hangi shugaban jam’iyar APC John Odigie-Oyegun yana shiga wurin taron.