Osinbajo ya gana da NAPTIP,NEMA kan yan Najeriya da suka makale a ƙasar LibyaMataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Laraba ya kira wani taro a Abuja na hukumomin da abin shafa domin tattauna halin da yan Najeriya ke ciki a kasar Libya.

An gudanar da taron ne a matsayin wani mataki na cika alkawarin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya ɗauka a Abidjan babban birnin kasar Cote d’Ivoire cewa gwamnatinsa zata kwaso yan Najeriya da suka makale a ƙasar Libya a ƙoƙarin da suke na zuwa nahiyar Turai.

Osinbajo ya gana da hukumar yaƙi da safarar mutane ta kasa NAPTIP, hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da kuma hukumar dake kula da yan gudun hijira domin su tattauna halin da ake ciki.

Ya kuma kara jaddada irin jajircewa gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari na ganin cewa matasa yan Najeriya sun daina jefa kansu cikin hatsarin dake tattare da tafiya a hamadar Sahara.

Osinbajo yace ya zama dole a fadakar da matasa yan Najeriya kan hatsarin dake tattare da keta tekun bahar Rum zuwa nahiyar Turai.

Yace y ana da muhimmanci akansu su sake duba halin da ake ciki kana sau ɗauki matakin kawo karshen lamarin.

You may also like