Mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ya gana da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma sarkin Kano Muhammad Sunusi II ranar Asabar a Kano.
Osinbajo ya ziyarci Kano ne domin halartar daurin auren , Hafiz Ibrahim ɗaya daga cikin masu taimaka masa.
Mataimakin shugaban ƙasar ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da misalin karfe 11:30 na safe.
Daga nan kuma ya zarce zuwa masallacin juma’a na Umar bin Khattab dake shatale-talen Dangi kan titin zuwa Zariya inda daurin auren ya gudana.
Bayan an gama daurin auren Osinbajo da Ganduje sun zarce zuwa fadar sarkin Kano.
ƴan mintoci kaɗan da isar su fadar mutanen uku suka shiga wata ganawar sirri da ta ɗauki tsawon mintuna 30.
Babu wata sanarwa da aka fitar kan abin da suka tattauna yayin ganawar amma wasu majiyoyi sun bayyana cewa ganawar na da alaƙa da rikicin dake faruwa tsakanin gwamna Ganduje da kuma tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso.