Osinbajo Ya Ziyarci Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Makurdi 


Yanzu haka Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo,yana can Makurdi babban birnin jihar Benue domin ganawa da mutanen da suka rasa mahallansu a bala’in ambaliyar ruwa da aka fuskanta a jihar.

 Osinbajo, wanda ya samu rakiyar wasu ministoci, ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai kai ziyara sansanin da aka tsugunar da mutanen da abin  ya shafa.

 Yana wakiltar shugaban kasa Muhammad Buhari ne wanda ya sha suka kan yadda yaki kai ziyarar gani da ido don ganin irin mummunar ta’adin da ambaliyar ta jawo.

Ambaliyar ruwan dai ta shafi gidaje da dama, kamfanoni har ma da wasu ma’aikatun gwamnati.

Dubban jama’a ne dai dmambaliyar ruwan ta raba su da mahallansu, suke kuma zaune a sansanonin da aka bude domin tsugunar dasu, inda suke zargin gwamnati da rashin basu kulawar da ta kamata.

You may also like