Osinbajo ya ziyarci Numan


Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yace gwamnatin tarayya zata nemi hanyar warware rikicin manoma da makiyaya a garin Numan.
Da yake magana a Numan yayin da yakai ziyara wasu daga cikin kauyukan da ake zargin Fulani makiyaya da kaiwa hari, Osinbajo yace ya fahimce cewa rikicin ya samo asaline daga dadaddiyar rashin fahimta da aka kasa magani tun a baya.

“Ziyara ta zuwa Adamawa shine fara wani tsari da zai kawo karshen wannan matsalar kwata-kwata. Dole mu nemi mafita ta dindindin akan wannan rikicin,” yace.

 Yayi kira da a kwantar da hankali da kuma yin amfani da tattaunawa wajen sasanta rikici tsakanin al’ummomi. Osinbajo ya jaddada kudurin gwamantin tarayya na kawo karshen rikicin.

” Wannan matsala ce ta mutane ba aljanu ne suka  haddasa ta ba saboda haka mutane ne za su magance ta.”

Hamma Bachama, Honest Irmiya Stephen,  basaraken gargajiya na garin ya koka kan rikicin da yadade yana addabar masarautarsa inda yayi kira da a sake tura karin  jami’an tsaro zuwa  yankin domin kare rayuka da dukiyar jama’a.Ya kuma yi kira da a dawo da ofishin shiya na yan sanda dake yankin wanda aka dauke daga garin a shekarar 2009.

You may also like