Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya umarci jagororin hukumomin tsaron kasar nan da su kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya a duk inda suke.
Umarnin shine martanin mukaddashin shugaban kasar kan wa’adin da wasu kungiyar matasan Arewa suka bawa al’ummar kabilar Igbo na su fice daga yankin kafin ranar 1 ga watan Oktoba.
Mai magana da yawun Osinbajo Laolu Akande ya bayyana haka a shafinsa na Twitter yau inda yace mai gidansa yabada umarnin ne a wani taro da yayi da jagororin hukumomin tsaron kasar nan a karshen mako.
“Mukaddashin shugaban kasa ya gana shugabannin hukumomin tsaro, a karshen mako ya kuma basu cikakken umarni kan su kare rayuka da kuma dukiyoyin yan Najeriya a duk inda suke,” Akande yace.
“Mukaddashin Shugaban kasa zai fara ganawa da shugabanni da suka fito daga yankin kudu maso gabas da kuma arewacin kasarnan yau da yamma.
” Da farko dai zai gana da shugabannin daban-daban kafin daga bisani ya gana dasu tare. “