Osinbajo Yakai Ziyarar Bazata Zuwa Kasuwar Garki Dake Abuja Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo yakai ziyarar bazata zuwa kasuwar Garki dake Abuja inda ya gana da wasu yan kasuwa dake gudanar da Sana’a, a kasuwar.

Mai magana da yawunsa, Laolu Akande yace ziyarar wani bangare ne na bukukuwan cikar gwamnatin Shugaban kasa Muhammad Buhari Shekaru biyu akan mulki. 

Yawancin yan kasuwa da Osinbajo ya gana dasu sun koka kan tsadar kudin hayar shago a kasuwar. 

Daya daga cikinsu Nasiru Kurfi, yace hukumomin kasuwar sun gaza kammala ginin shagunan da yan kasuwar suka biya kudinsu shekaru da suka wuce.

 Osinbajo ya samu rakiyar karamar ministar ciniki da magana’antu da zuba jari, Hajiya Aisha Abubakar, ya roki an kasuwar da su saukaka farashin kayansu musamman ma a cikin watan Ramadan. 

 Mai rikon mukamin Shugaban kasar ya kuma shawarci yan Najeriya da su koma noma ,inda yace “Yawan abincin da muka noma shi zaisa farashin abinci yayi kasa. ”

 

Mai magana da yawunsa ya fadawa yan jaridun da suke dauko rahoto daga fadar Shugaban kasa cewa shugaban ya ziyarci kasuwar ne domin yaji irin halin da mutane suke ciki. 

You may also like