A jiya lahadi ne wato 25/6/2017, kamfanin yada labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa Mukaddashin shugaban kasa, prof Yemi Osinbajo yayi wata ganawar sirri da shugaban kasar Ghana Akufo-Addo.
Rahotannin sun nuna cewa, sun gana ne a Aguda Housa dake fadar Shugaban kasar Nigeria inda aka tabbatar da cewa sun tattauna har tsawon sama da sa’a daya.
Musabbabin ganawar tasu ne har yanzu ba’a sani ba.