Osinbanjo ya gana da su Saraki, Kwankwaso, Dogaro da sauran tsofaffin yan jam’iyar PDP


Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo ya gana da yayan jam’iyar APC wadanda suka shigo jam’iyar daga PDP da sukaiwa kansu lakabn nPDP a baya

Taron ya gudana ne a gidan mataimakin shugaban kasa da ake kira Aguda House dake fadar shugaban kasa.

Mataimakin shugaban jam’iyar APC na kasa Lawal Shuaibu da kuma ministan shari’a Abubakar Malami na daga cikin wadanda suka halarci zaman taron.

Yan banagaren sabuwar PDP da suka halarci zaman tattaunawar sun hada da Bukola Saraki, Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmad da kuma tsohon gwamnan jihar.

Sauran sune, Danjuma Goje, sanata Barnabas Gemade da kuma wasu yan majalisar wakilai.

A kwanakin bayane mutanen suka rubuta wasika ga shugaban kasa Muhammad Buhari inda suke nuna yadda aka mayar da su saniyar ware duk da gudunmawar da suka bayar wajen kafa gwamnati.

You may also like