Oyegun ya gana da Saraki da kuma sanatoci yan jam’iyar APC


John Odigie Oyegun, shugaban jam’iyar APC na kasa a yanzu haka yana ganawa da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kuma sanatoci da suka fito daga  jam’iyar.

Oyegun ya je majalisar ne tare da dukkanin yan kwamitin gudanarwa na jam’iyar.

Da yake magana kafin su shiga ganawar sirri a ranar Laraba, Oyegun ya ce sun kasance a majalisar ne domin su ” tattauna, saurara kana su kara shiri,”kafin zaben shekarar 2019.
Shugaban na APC ya ce za a tattauna “batutuwa ” a wurin taron.

“Mun zo nan mu tattauna batutuwa , za mu fuskanci zabe kasa da shekara guda mai zuwa,”Oyegun ya ce.

Oyegun ya kuma yi wa yan majalisar ta’aziyar abokin aikinsu da ya rasu, Sanata Ali Wakili

You may also like