Ozturk ya amsa laifin juyin mulkin Turkiya


Tsohon kwamandan sojin saman Turkiya Janar Akin Ozturk ya amsa laifin shirya juyin mulkin da bai yi nasara ba ranar juma’a.

Janar Ozturk ya shaida wa masu yi masa tambayoyi cewar da sanin sa ya shirya juyin mulkin.

A baya dai Janar din yaki amincewa da zargin da aka masa tare da wasu Janar Janar guda 20 da aka kama yanzu haka.

Mahukuntan Kasar sun sanar da kama kimanin mutane dubu 6 ake zargi da yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Recep Tayyip Erdogan.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like