
Asalin hoton, Getty Images
Pakistan ta toshe shafin Wikipedia saboda wallafa wasu bayanai na ‘ɓatancin ga addini’.
An bayyana matakin ne ranar Asabar bayan wa’adin – kwanaki biyu da aka bai wa shafin yanar gizon na encyclopaedia ya cire wasu bayanai a shafin – ya cika.
Hukumar sadarwar ƙasar ta ce shafin na Wikipedia ya gaza bin umarnin da aka ba shi kafin cikar wa’adin.
Gidauniyar Wikimedia, wanda ke da mallakin shafin na Wikipedia, ya ce matakin toshe shafin na nufin haramta wa al’ummar Pakistan samun ilimi ”kyauta daga ƙaton rumbun ilimin”.
Ɓatanci ko saɓo babban laifi ne da zai iya janyo rikici a Pakistan.
A baya dai ƙasar – wadda ke da rinjayen musulmi – ta taɓa toshe wasu kafofin sadarwa kamar shafukan Tinder da Facebook da kuma Youtube.
Mai magana da yawun hukumar sadarwar ƙasar Malahat Obaid ya ce shafin na Wikipedia ya gaza ɗaukar mataki game da abubuwan da aka nusar da shi a kansu na ‘ɓatanci’.
“Sun cire wasu daga ciki amma ba duka ba” in ji shi, inda ya tabbatar da cewa shafin zai ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa lokacin da zai cire duka ”abubuwan da aka nusar da shi a kansu”.
To sai dai ba a yi cikakken bayani kan abubuwan ɓatancin da shafin ya wallafa ba.
To sai dai gidauniyar Wikimedia ta ce idan haramcin ya ci gaba hakan zai ”hana kowa samun ilimi game da tarihi da al’adun Pakistan”.
Masu fafutikar kare hakkin bil-adama sun bayyana damuwa game da matakin, suna masu cewa matakin tamkar ”yunƙurin samun iko ne ga abubuwan internet”.
“Babban dalili shi ne saboda shirun da ake yi ne,” in ji Usama Khilji wani mai sharhi game da shafukan internet.
“A lokuta da dama ana amfani da kalmar ‘ɓatanci’ a matsayin makamin ƙuntata wa mutane,” in ji shi.
A shekarar 2010 Pakistan ta toshe shafin YouTube saboda da ƙaruwar ”abubuwan saɓo a shafin”.
An kuma toshe shafin Facebook a shekarar ta 2010 bayan da aka yi ta samun gangamin kiraye-kirayen zana hotunan Annabi Muhammad (S.A.W) a shafin.
Haka kuma a bayan an toshe shafukan Tinder da Grinder sakamakon yaɗa ‘abubuwan da suka saɓa wa addini’ a ƙasar.