Paparoma Francis ya damu da rikicin Isra’ila da Falasdinawa | Labarai | DWJagoran darikar Katolika na duniya Paparoma Francis, ya soki yadda tashe-tashen hankula a Ukraine da Gabas ta Tsakiya da hare-haren ta’addancin duniya a matsayin abinda ke mayar da hannun agogo baya ga zaman lafiyar duniya.

A gaban dandazon mabiya darikar Katolika kimanin dubu 100 a wannan Lahadi, babban limamin mabiya addinin Kiristan ya nuna damuwa kan rikicin da ya kunno kai tsakanin Isra’ila da Falasdinu, lamarin da ya kira mummunar barazana ga kokarin sulhunta rikicin bangarorin biyu.

Kana Paparoma Francis, ya nuna alhini ga wadanda suka rasa danginsu a yankin Ukaraine da ma masu yin hijira, tare da mika kira ga kasashen duniya da su yi mai yiwuwa don tabbatar da dorewar zaman lafiya a doron kasa. Babban limamin na jawbin ne, a albarkacin bukuwan Earster na wannan shekara.

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like