Patience Jonathan Ta Nemi Sulhu Da EFCC Kan Dala Miliyan 15


Uwargidan Tsohon Shugaban Kasa, Patience Jonathan ta nemi sulhu da hukumar EFCC kan Dala milyan 15 da hukumar ke zargin kudaden gwamnati da aka sace ta hanyar amfani da gidauniyar Uwargidan tsohon Shugaban .

Rahotanni sun nuna cewa lauyan Patience Jonathan ya nemi EFCC ta janye karar da shigar kotu na neman a mallakawa gwamnatin wadannan kudaden sai dai kuma wata majiya daga EFCC ta nuna cewa hukumar ba za ta amince da wannan tayin ba saboda tana da kwararan shaidu kan wannan zargin. A shekarar da ta gabata ne dai, EFCC ta rufe wasu asusun ajiyar Bankin Uwargidan Jonathan din.

You may also like