Patience Jonathan ta yi Rubuta wasika ga hukumar EFCC .


Patience Jonathan tayi rubuta wasika ga Ibrahim Magu, shugaban hukumar yaki da cin hanci darashawa (EFCC) ta bayyana cewa kudi dala miliyan 3.41 dake cikin asusunta kudin kiwon lafiyarta ne.

Matar tsohon shugaban kasar da farko ta yi shirin kai  karar hukumar yaki da cin hanci da rashawa bayan sun kwashe kudin da ke asusun ta.Jaridar Guardian ta ruwaito cewa an bayyan aasusun a daya daga cikin wadanda ake zargin suna  da hannu a cikin zamba a gaban wani babban kotun tarayya dake jihar Lagas, amma mai ba Mrs Jonathan shawara, Gboyega Oduwole ta kai lamarin gaban wani kotu, tana bayanin cewa abokiyar harkarta bata ji dadin abinda hukumar EFCC ba.

Rahotanin nanuna cewa Patience ta canza tsari a yanzu ta kuma rubuta wasika ne kai tsaye zuwa ga shugaban hukumar EFCC ta bukaci a  dawo mata da kudin dake asusunta.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like