Pauline Tallen ta warke daga cutar Korona


Ministar harakokin mata ta Najeriya,Pauline Tallen ta warke daga cutar Korona.

Ministar ta sanar da haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin a Abuja.

Tallen ta shawarci yan Najeriya da su bi ka’idodin da aka shinfida dan gudun kada su kamu da cutar ta kuma godewa baki dayan matan Najeriya kan addu’ar da suka yi mata.

Ta yi alkawarin cigaba da bijiro da ayyuka da za su inganta rayuwar matan Najeriya.

You may also like