Tsohon shugaban kasa Gudluck Jonathan yace PDP ce jam’iya kaɗai da bata yaudari yan Najeriya ba.
Da yake magana a wurin babban taron zaben shugabannin jam’iyar. Jonathan ya ce PDP jam’iya ɗaya da ta zauna da ƙafafuwanta.
Toshon shugaban kasar yace jam’iyar tayi abin a yaba a tsawon lokacin da ta kwashe tana mulkin kasarnan.
Ya ce jam’iyar PDP ce kaɗai bata da sauya suna ba daga sunan da aka sanya da shi tun lokacin da aka kafata kawo yanzu.
A yau ranar Asabar 9 ga watan Disamba d jam’iyar ta PDP ke gudanar da babban taron ta na kasa inda take zabar shugabanni da za su jagoranci jam’iyar.
Sai dai tun a jiya aka fara samun sabani inda daya daga cikin yan takarar Olabode George ya bada sanarwar ficewa daga zaben bisa zargin yunkurin da wasu mutane keyi na kakaba yan takara akan ya’yan jam’iyar.