PDP basu yadda da sakamakon zaben jahar Edo ba


Jam’iyar PDP basu yadda da sakamakon zaben jahar Edo ba na gwamna wanda a halin yanzu hukumar zabe me zaman janta INEC ke sanar wa.

Lokacin da yake tattaynawa da manema labarai, shugaban jam’iyar PDP Dan Obih, yace sakamakon da wakilan mu na kowace rumfa suka kawo mana a daren jiya ya banbanta da abunda hukumar zabe ke sanar wa.

Ya kara da cewa wanda sabanin cewan da akayi mun kawo yan ta’adda 8000,, ya nuna kamar ba wani abu da ya faru, tsaikon da aka samu na sanar da sakamakon daga INEC ya nuna sakamakon an riga anyi shi kuma an rubutashi.

 

Abunda ake sanarwa ya saba da saba da yawan mutanen da suka fito jefa kuri’a, kuma nasan ko Shugaban jam’iyar APC na kasa ya fahim ci, amma ina fada maku lokacin da INEC ke fadin sakamakon ya saba da yawan fitowar mutane lokacin zaben.

 

 

 

 

Iza – Iyan dan takarar gwamna a jam’iyar yace” APC ba zasu iya cin karamar hukumar Oredu ba duk da shaidun rigime-rigemen da yan ta’addan APC  sukayi a rumfar wanda yaja soke rumfar.

Da aka tambaye shi meye matakin da zasu dauka, sai yace zamu rubuta mu saka a jarida samakon da ya dace ace an gani.

Yayan jam’iyar sun fito a safiyar yau suna yin zanga-zanga a gaban ofishin hukumar zabe ta jahar. A wata majiya kuma munji cewa dan takarar jam’iyar APGA ta nemi da a soke zaben na jahar Edo.

Yace yadda mutanen Edo suka fito ta kayatar, mutanen Edo suna bukatar canji, yace zaben yana cike da hargitsi.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like