PDP ce ta Durkusar da Nigeria –  APC


 

 

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce Jam’iyyar adawa ta PDP ce ke da alhakin tabarbarewar da tattalin arzikin kasar ya shiga.
APC na mayar da martani ne dangane da sanarwar da PDP ta fitar inda ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya yi murabus saboda gazawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar.

Sakataren Jam’iyyar APC na kasa Alhaji Mai Mala Buni a wata sanarwa, ya ce PDP ba ta da kima da har zata rika sukar salon mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

A cewar APC, kamata ya yi PDP ta nemi afuwar ‘yan Najeriya saboda halin da ta jefa kasar a ciki a tsawon shekaru goma sha shida da jam’iyyar PDP ta shafe tana mulkin kasar, maimakon neman shugaba Buhari ya yi murabus.Jam’iyyar APC ta kara da cewa irin tsare-tsaren tattalin arzikin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta bullo da su za su taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasar daga mawuyacin halin da yake ciki.

You may also like