PDP  Na Addu’ar Warkewar Shugaban Kasa Buhari – Makarfi   


Shugaban jam’iyar PDP na kasa, sanata Ahmad Muhammad Makarfi, yace jam’iyar zata cigaba da yiwa shugaban kasa Buhari addu’ar samun lafiya.

A wurin babban taron jam’iyar na kasa a Abuja,Makarfi yace  samun lafiyar shugaban kasar na daga cikin abinda jam’iyar PDP take so kuma take fata. 

“Muna fatan alkhairi ga shugaban kasar, zamu cigaba da yi masa addu’a, muna so ya warke sumul amma hakan ba yana nufin zamu je muyi bacci bane a’a , zamu yi aiki tukuru domin cin zaben 2019,”yace.

Ya bayyana babban taron jam’iyar wanda bana zaben shugabanni bane a matsayin wata manuniyya dake tabbatar da PDP a matsayin gwamnati mai jiran gado.

   Makarfi ya yabawa jami’an tsaro kan yadda suka tabbatar an gudanar da zaben lami lafiya.

 Ya kuma yabawa hukumar zabe ta kasa INEC kan yadda take gudanar da aikinta ba tare da nuna banbanci ba. 

You may also like