PDP Na Shirin Daukaka Kara Kan Hukuncin Da Kotun Sauraren Kararrakin Zabe Ta Yanke A Jihar Filato
A makon jiya ne mai shara’a B.M. Tukur dake jagorantar wata kotun sauraron kararrakin zabe a jihar Filato ta karbe takardar shaidar yin nasarar zabe na sanata daga kudancin jihar Filato, Air Vice Marshal, Napoleon Bali ta baiwa Ministan kwadago, Simon Lalong na APC.

Kazalika kotun ta karbe nasarar wasu ‘yan majalisun tarayya da suka hada da Beni Lar, Musa Bagos da Peter Gyendeng wadanda dukkansu ‘yan jami’iyyar PDP ne.

Alkalin kotun, mai shara’a B.M. Tukur ya kafa hujjojin rashin tsari wato zababbun shugabanni da PDPn da ba ta da shi gabanin gudanar da zaben da kuma bijire wa umurnin kotu wajen zaben shugabannin jami’iyya kafin gudanar da zaben gama gari.

Kakakin jami’iyyar PDP a Jihar Filato, Mr. John Akans, ya ce a baya PDP a jihar ta sami matsalar shugabanci amma daga bisani ‘ya’yanta sun sasanta kuma ta gudanar da zaben shugabannin da sanin hukumar INEC da jami’an tsaro, kafin zaben na gama gari.

Honarabul Abdullahi Chiroma, na jami’iyyar PDP a Jos ta Arewa, ya ce ba su fahinci yadda kotun ta amince da kujerun wasu ‘yan jami’iyyar PDPn ta kuma yi watsi da na wasu ba.

Shi ma Nuhu Jafaru wanda ya yi takarar kansila a Ibrahim Kazaure Ward da ke karamar hukumar Jos ta Arewa, karkashin lemar PDP ya ce shara’ar ta kasance sabanin hankali a wurinsu.

Lauyan jami’iyyar PDP a jihar Filato, Barista Fwangshak Bitrus, ya tabbatar da cewa PDP ta gudanar da zaben shugabanninta kafin zabe.

Ya zuwa yanzu dai jama’ar jihar na hankoron sauraron hukuncin kujerar gwamna da na ‘yan majalisun dokoki wanda kotun ba ta sanar da rana ba.

Saurari rahoton:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like