PDP Reshen Jihar Sokoto Ta Yi Wa Al’ummar Wamakko Ta’aziyar Rasuwar Barade JabbiShugaban jam’iyyar PDP na jahar Sokoto Alh Ibrahim Milgoma ya jagoranci wani ayarin shugabanin jam’iyyar PDP na jaha don gabatar da ta’azziya ga al’ummar yankin karamar hukumar mulkin Wamakko dake jahar Sokoto dangane da rasuwar Baraden Wamakko Malam Abubakar Jabbi wanda ya rasu a jiya Jumu’a sakamakon wata gajeruwar rashin lafiya. 

A lokacin ziyarar Alh. Ibrahim Milgoma ya kaiwa  Baraden Wamakko Alh. Salihu Barade gaisuwa ta’azziya kamin yiwa iyalan marigayi Baraden tasu ta’azziya gidansu dake garin na Wamakko. 

Alh. Ibrahim Milgoma ya kuma gabatar da sakon ta’azziya na tsohon gwamna jahar Sokoto Alh. Attahiru Bafarawa ga ilalhirin yan uwa da makusantan mamacin. 
Milgoma ya baiyana Marigayi Barade Jabbi da kasancewa mutum mai son gaskiya da rikon amana tare da zumunci abin da ya sanya rasuwar ta kasance babban rashi ga iyalansa da sauran al’ummar Musulmi baki daya. 

Marigayi Abubakar Jabbi wanda ya shekara fiye da takwas baya akan karagar mulki ya rasu da shekaru 88 a duniya. 

Sauran wadanda suke cikin tawagar shugaban jam’iyyar PDP akwai mataimakinsa Alh. Yahaya Nasani Danmaliki Isa da Alh. Kabir Aliyu Sakataren jam’iyyar da Alh. Yusuf Dingyadi Sakataren Watsa Labarai na jam’iyyar da Alh. Kasimu Dangaladiman Jarman Sokoto da Alh. Sani Bado da shugabanin jam’iyyar na yankunan Sokoto ta Arewa da Kudu da Kware.

Baraden Wamakko na 11 wanda Gwamnatin Aliyu Magatakarda Wamakko ta cire bisa sarauta shekaru kusan takwas da ta gabata ne ya rasu.

You may also like