PDP Reshen Kaduna Ta Tsayar Da Makarfi A Matsayin Dan Takarar Shugaban Ƙasa


Jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta tsayar da tsohon Gwamnan jihar, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi a matsayin dan takarar Shugaban kasa na zaben 2019.

Shugabannin gudanarwa na jam’iyyar sun nuna cewa Makarfi ne kadai ya fi cancanta ya fafata da Shugaba Buhari saboda kwarewarsa kan Harkokin mulki da na siyasa.

You may also like