PDP –  Sheriff da Makarfii zasuyi sulhu


Mutum biyu da ke kokawar shugabancin jam’iyyar PDP a Najeriya, Sanata Ahmed Makarfi da Sanata Ali Modu Sheriff sun sha alwashin sasantawa.
Mutanen dai sun dade suna ja-in-ja game da shugabancin jam’iyyar, lamarin da ya kai su ga kotuna daban-daban.

Sai dai bangarorin biyu sun shaida wa ‘yan jaridu  cewa za su sasanta da juna domin kawo karshen kai-ruwa-ranar da suka kwashe wata da watanni suna yi.

Jam’iyyar ta PDP dai ta fada cikin rikici ne tun bayan kayen da ta sha a zaben shugaban Najeriya na shekarar 2015.

Masu sharhi a kan harkokin siyasar kasar sun ce rashin hada kai tsakanin ‘yan jam’iyyar ta PDP wani babban koma-baya ne ga dimokradiyya kasancewa babu jam’iyyar da za ta soki gwamnatin kasar wacce ta kwace mulki daga PDP.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like