A yayin wata tattaunawar sa da Wakilin mu a filin taron zaben sabbin shuwagabannin jam’iyyar da ya gabata shekaran jiya a Abuja ga abinda Atikun yake cewa.
“Wannan zaben da akayi ya ishemu hujja cewa Yanzu ba da ba ne domin tun da aka halasci PDP ba’a taba yin zabe Mai inganci irin wannan ba duk Wanda kaga yana sukar wannan zabe to bai kishin jam’iyya.
A don haka muke kira ga ‘yan najeriya da suzo mu hada hannu domin ciyar da kasar nan gaba.” Inji Atiku