PDP Ta Kalubalanci Majalisa Kan Ta Binciki Yadda Aka arce Da Ƴan Matan Dapchi


Jam’iyyar adawa ta PDP ta kalubalanci majalisar tarayya kan ta gaggauta gudanar da bincike kan yadda mayakan Boko Haram suka samu nasarar arcewa da daliban Sakandaren mata na Dapchi da ke jihar Yobe har su 110.

Sakataren Hulda da Jama’a na jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ya ce gudanar da binciken ya zama dole ganin yadda bangarorin da abin ya shafa ke ci gaba da dorawa juna laifin faruwar al’amarin musamman ma yadda Gwamnan Yobe ya fito fili ya zargi sojoji kan Janyewa daga yankin wanda hakan ya ba ‘yan Boko Haram damar shiga makarantar.

You may also like