
Asalin hoton, FACEBOOK/Umar Iliya Damagum
Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP ya amince da nadin Ambasada Umar Iliya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa.
A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar bayan ganawar gaggawa da kwamitin gudanarwar PDP na ƙasa ya gudanar ranar Talata, ta ce ta ɗauki matakin ne domin biyayya ga hukuncin da babbar kotun jihar Benue ta yanke game da matayin shugabancin Iyochia Ayu.
Da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron a shalkwatar PDP ta ƙasa, sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Debo Ologunagba, ya ce bayan nazari a kan hukuncin kotun da kuma la’akari da sashe na 45 (2) na tsarin mulkin PDP, kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya amince da naɗa mataimakin shugaban PDP mai kula da shiyyar arewacin ƙasar, Amb. Umar Ililya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar.
Matakin na zuwa ne bayan, babbar jam’iyyar adawar ta Najeriya ta sanar da dakatar da Dr Iyorchia Ayu, bisa zargin sa da wasu ayyuka na cin amana. Shugabannin PDP a matakin gundumarsa da ke ƙaramar hukumar Gboko cikin jihar Benue ne suka ɗauki matakin dakatar da shi.
Sun ce sun dakatar da shi ne bayan sun kaɗa ƙuri’ar dawowa daga rakiyar shugabancinsa. A lokacin da ya karanta matsayar da shugabannin suka cimma, sakataren jam’iyyar a gundumar Igyorov, Vanger Dooyum ya ce zagon-ƙasa da Ayu da kuma makusantansa suka yi wa PDP ne ya janyo mata faɗuwa a zaɓe cikin gundumar da kuma jihar Binuwai baki ɗaya, a zaɓen gwamna.