PDP ta nemi yan Najeriya su bijirewa duk wani yinkurin gwamnati na kara kuɗin mai


Jam’iyar PDP ta yi kira ga yan Najeriya da su bijirewa duk wani shiri da gwamnatin tarayya ke dashi ma kara farashin kuɗin mai.

Akwai rahotanni da ke cewa gwamanti mai ci na shirin kara kuɗin mai amma kuma karamin ministan albarkatun mai, Ibe Kachikwu ya tabbatarwa da yan Najeriya cewa farashin litar mai zai cigaba da zama ₦145 kan kowace lita.

Kola Ologbodiyan mai magana da yawun jam’iyar PDP ya ce duk wani yunkuri na ƙara kuɗin mai zai kasance “babu tausayi kuma baza a amince da shi ba.”

Yakara da cewa kara kuɗin  mai zai zama ɗorawa tamkar an ɗorawa dukkan yan  Najeriya haraji ne  a fakaice inda yace hakan zai ƙara jefasu cikin wahala.

Yayi kira da gwamnatin kan ta fito tayi karin haske kan “biyan kuɗin tallafin mai”a karkashin wannan gwamnati.

You may also like