PDP ta sake tsunduma cikin rikici


sheriff-makarfi-pdp

Kwanaki kadan bayan sulhu a tsakaninsu, bangororin da suke rikici kan shugabancin jam’iyar adawa ta PDP sun sake tsunduma cikin rikici.

Rikicin na baya bayan nan ya samo asaline bayan da bangaren shugabancin ALi Modu Sharif yayi yunkurin musanya ma’aikatan dake sakatariyar jam’iyar ta kasa, wadanda ya zarga da kin goya masa baya ya gudanar da aikinsa.

Shareef ya bayyana  ma’aikatan a matsayin korarru yayin da ya umarcesu dasu dawo da kayayyakin jam’iyar da yake hannunsu batare da bata lokaci ba.

Sai dai kuma bangaren shugabancin Ahmad Makarfi yayi kira ga ma’aikatan da suyi watsi da barazanar da Sharif yayi musu.

” Barazanarsa akan jajirtattun ma’aikatan mu da suke aiki tukuru abun a yi watsi da ita ne ,kuma ya zama dole a bijire mata tunda ta fito ne daga bakin mutumin da ba shugabane na hakika ba,  wanda kuma baya bin  doka” a tabakin Dayo Adeyeye jami’in yada labaran jam’iyar bangaren Makarfi wanda ya mayar wa da Sharif martani.

A ranar Alhamis ne Sharif da Makarfi suka sa hannu kan wata yarjejeniya daza ta kawo karshen rikicin da ya dabaibaye jam’iyar ta PDP.

Sai dai ajiya lahadi ALi Modu sharif ya bayyana cewa shugabancin Makarfi  ba halattace bane,tun bayan hukuncin da kotun daukaka kara dake Fatakwal ta yanke ranar 17 ga watan Faburairu.

Yayi kira da kafafen yada labarai da sune daina kiran bangaren Makarfi a matsayin wani tsagi na PDP, inda ya jaddada cewa shugabancinsu ba halattace bane.

Jam’iyar ta PDP ta dade tana fama da rikici tun bayan kayin da ta sha a zaben 2015 a hannun Jam’iyar APC.

 

You may also like