PDP ta yi barazanar maka gwamnatin Kano gaban kotu 


Jam’iyar PDP a jihar Kano ta yi barazanar daukar matakin shari’a akan gwamnatin jihar Kano kan zargin da take yi wa gwamnatin na yin amfani da jami’an yan sanda wajen hana ta yin taron gangamin da ta shirya yi a karamar hukumar Gaya dake jihar.

Shugaban jam’iyar na jihar, Alhaji Mas’ud El-Jibril Doguwa shine ya bayyana matsayin jam’iyar lokacin da yake wa manema labarai jawabi ranar Juma’a a Kano.

Ya ce ya yin taron gangamin jam’iyar ta shirya karbar dantakarar gwamna a karkashin jam’iyar PDM a zaben shekarar 2015,Engr. Bashir Ishaq da kuma magoya bayansa ya zuwa cikin jam’iyar PDP.

Ya ce domin girmamawa a hukumance da kuma tabbatar da cikakken tsaro jam’iyar ta rubuta takarda ga dukkanin hukumomin tsaro da abin ya shafa ciki har da rundunar yan sandan Najeriya da kuma hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS makonnin da suka wuce.

Ya kara da cewa dukkanin hukumomin tsaron sun tabbatarwa da jam’iyar hadin kansu hakan ya basu kwarin gwiwar cigaba da shirye-shiryensu.

Doguwa ya ce kawai a jiya ranar Alhamis sai suka samu takarda daga rundunar yan sanda kan su janye taron da suka shirya yi saboda abinda suka kira “matsalolin tsaro.”


Like it? Share with your friends!

0

You may also like