An bayyana Uche Secondus a matsayin sabon shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP, a babban taron da aka tsawon daren Asabar bayan an gama kidaya kuri’u.
Da yake sanar da sakamakon zaben, shugaban kwamitin zabe, Mista Gabriel Suswam, ya ce Uche Secondus ya kayar da abokan takararsa uku bayan ya samu kuri’a 2000.
Haka zalika, an zabi Sanata Umar Ibrahim a matsayin sabon Sakataren jam’iyyar na kasa, kuma tuni aka rantsar da sabbin shugabannin don kama aiki.
Mahalarta babban taron dai sun zabi sabbin jami’an da za su ja ragamar jam’iyyar kan mukamai guda 21 ne.
Tun da farko dambarwa ta kunno kai bayan wasu sun yi zargin shirya magudi, lokacin da wata takarda ta rinka zagaya hannun mahalarta taron