Rahotanni daga Rivers sun tabbatar da cewa Jam’iyyar PDP ce kan gaba a zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar a bisa sakamakon kuri’un da hukumar zabe mai zaman kanta ta fitar a halin yanzu.
Tuni dai, PDP ta samu lashe kujerar dan majalisar wakilai. An dai samu hatsaniya a yayin gudanar da zaben inda akalla mutane uku suka rasa rayukansu baya ga rahotanni arcewa da kayayyakin zabe a wasu rumfunar zabe da duk da yawan jami’an tsaro da aka girke a fadin jihar.